Matthew 23

Laʼanu Bakwai

1Saʼan nan Yesu ya ce wa taron mutane da kuma almajiransa: 2“Malaman dokoki da Farisiyawa suke zama a kujerar Musa. 3Saboda haka dole ku yi musu biyayya, ku kuma yi duk abin da suka faɗa muku. Sai dai kada ku yi abin da suke yi, gama ba sa yin abin da suke waʼazi. 4Sukan ɗaura kaya masu nauyi, su sa wa mutane a kafaɗa. Amma su kansu, ba sa ko sa yatsa su taimaka.

5“Kome suke yi, suna yi ne don mutane su gani: Sukan yi layunsu fantam-fantam
Wato, akwatuna kunshe da ayoyin Nassi, da suke ɗaura a goshinsu da kuma hannuwansu
bakin rigunarsu kuma sukan kai har ƙasa;
6suna son wurin zaman manya a wurin biki, da kuma wuraren zama gaba gaba a majamiʼu; 7suna so a yi ta gaisuwansu a kasuwa, ana kuma riƙa ce musu, ‘Rabbi.’

8“Amma kada a kira ku ‘Rabbi,’ gama kuna da Maigida ɗaya ne, ku duka kuwa, ʼyanʼuwa ne. 9Kada kuma ku kira wani a duniya ‘uba’, gama kuna da Uba ɗaya ne, yana kuwa a sama. 10Ba kuwa za a kira ku ‘malam’ ba, gama kuna da Malami ɗaya ne, Kiristi. 11Mafi girma a cikinku, zai zama bawanku. 12Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi, duk kuma wanda ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.

13“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kun rufe mulkin sama a gaban mutane. Ku kanku ba ku shiga ba, ba kuwa bar waɗanda suke ƙoƙarin shiga su shiga ba.
Waɗansu rubuce rubucen hannu na dā suna da zuwa. 14 Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, ku munafukai! Kukan ƙwace gidajen gwauraye, kuma don nuna iyawa, sai ku yi dogayen adduʼoʼi. Saboda haka za ku sha hukunci mai tsanani.


14
This verse is empty in this translation.
15“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan yi tafiye tafiye zuwa ƙasashe, ku ƙetare teku don ku sami mai tuba ɗaya, saʼad da ya tuba kuwa, sai ku mai da shi ɗan wuta fiye da ku, har sau biyu.

16“Kaitonku, makafi jagora! Kukan ce, ‘In wani ya rantse da haikali, ba damuwa; amma in ya rantse da zinariyar haikali, sai rantsuwar ta kama shi.’ 17Wawaye makafi! Wanne ya fi girma: zinariyar, ko haikalin da yake tsarkake zinariyar? 18Kukan kuma ce, ‘In wani ya rantse da bagade, ba damuwa; amma in ya rantse da bayarwar da take bisansa, sai rantsuwar ta kama shi.’ 19Makafi kawai! Wanne ya fi girma: bayarwar, ko kuwa bagaden da yake tsarkake bayarwar? 20Saboda haka, duk wanda ya rantse da bagade, ya rantse ne da bagaden tare da abin da yake bisansa. 21Kuma duk wanda ya rantse da haikali, ya rantse ne da shi da kuma wanda yake zaune a cikinsa. 22Duk kuma wanda ya rantse da sama, ya rantse ne da kursiyin Allah da kuma wanda yake zaune a kansa.

23“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan ba da kashi ɗaya bisa goma na kayan yajinku-naʼanaʼa, anise, da lafsur. Amma kun ƙyale abubuwan da suka fi girma na dokoki-adalci, jinƙai da aminci. Waɗannan ne ya kamata da kun kiyaye ba tare da kun ƙyale sauran ba. 24Makafi jagora! Kukan tace ƙwaro ɗan mitsil amma sai ku haɗiye raƙumi.

25“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan wanke bayan kwaf da kwano, amma a ciki, cike suke da zalunci da sonkai. 26Kai makaho Bafarisiye! Ka fara wanke cikin kwaf da kwano, saʼan nan bayan ma zai zama da tsabta.

27“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kuna kama da kaburburan da aka shafa musu farin fenti, waɗanda suna da kyan gani a waje, amma a ciki, cike suke da ƙasusuwan matattu da kuma kowane irin abu mai ƙazanta. 28Haka ku ma, a waje, a idon mutane, ku masu adalci ne, amma a ciki, cike kuke da munafunci da mugunta.

29“Kaitonku, malaman dokoki da Farisiyawa, munafukai! Kukan gina kaburbura don annabawa, ku kuma yi wa kaburburan mutane masu adalci ado. 30Kuna cewa, ‘Da mun kasance a zamanin kakanninmu, ai, da ba mu haɗa hannu da su muka karkashe annabawa ba.’ 31Ta haka kuna ba da shaida a kanku cewa ku zuriyar waɗanda suka karkashe annabawa ne. 32To, sai ku cikasa zunubin kakanninku!

33“Ku macizai! ʼYaʼyan macizai! Ta yaya za ku tsere wa hukuncin jahannama ta wuta? 34Saboda haka ina aika muku da annabawa, da masu hikima da malamai. Waɗansunsu za ku kashe ku kuma gicciye; waɗansu kuma za ku yi musu bulala a majamiʼunku kuna kuma binsu gari gari. 35Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku. 36Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani.

37“Ayya Urushalima, Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ʼyaʼyanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ʼyaʼyanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi. 38Ga shi, an bar muku gidanku a yashe. 39Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’
Zab 118.26


Copyright information for HauSRK